Ko KunSan Berayen Nigeria? 


Wadannan sune Sunayen ƁERAYEN Da Suka Talauta Nijeriya su ake Tunanin Sune Sula na Matsalar Tattalin Arzikin da Najeriya Take ciki  a Yanzu. 
1…Alex Badeh ya haka rami ya binne Dala miliyan talatin da biyu a gidansa….$32 million dollars
2…An ba wa ɗan daba Tompolo Naira Biliyan Goma sha uku daga hukumar (Nimasa) N13billion saboda ya gina Jami’a a yankin Niger Delta 
3… Naira Miliyan Dari tara da hamsin (N950 million) aka rarraba a gidan -Shekarau
4… Mai gidana yace in karbo Dala miliyan Goma sha daya daga Babban Bankin Nijeriya  CBN ($11 million )…Dasuki Account Officer
5… Shugaban Kasa Yace in canza zunzurutun kudi har Naira Biliyan Goma (N10b) zuwa kudaden kasashen waje. Don a rabawa Delegates din Jam,iyyar PDP….. Dasuki
6…Na bada Naira Miliyan 100 ga odili, Jim Nwobodo, Bode George da sauransu…..Yuguda….
7… Na karbi Naira Biliyan Biyu da miliyan Dari( N2.1b) daga wajen Daauki saboda watsa Labarai…Dokpesi
8…Na Karbi Naira miliyan dari shida da hamsin (N650m) daga wajen Dasuki, saboda gyara ofis dina daya kone a abuja…..Thisday Obaigbena
9… Na karbi Naira miliyan dari uku da hamsin (N350m) daga wajen Dasuki don tattaunawa da manema labarai – Iyorchia Ayu
10… Na Karɓi Naira biliyan uku (N3b) daga wajen Dasuki don rabawa malamai su yi Addu’a….Bafarawa
11… Naira biliyan goma sha biyu kudaden fanshon yan sanda….12.7b
12… Bode-George tare da  Dabo sun karbi Naira biliyan Dari…..N100b
13…Olisa Metuh ya karbi Naira miliyan dari hudu  (N400 million)
14… Aziboala, ɗan uwan shugaba Goodluck ya karbi Naira biliyan shida…( N6 billion naira)
15…Tony Anenih ya karbi Naira miliyan dari hudu (N400 million )
16…Lucky Igbinedion ya karbi Naira biliyan goma sha shida (N16 billion) 
17…Tsohon shugaban sojojin sama Amosu ya handame naira biliyan biyu..(N2 billion naira)
18…Pastor Ayo Oritsejafor ya hadiye Dala miliyan talatin da biyar kudin siyo makamai ( $35 million dollars)
19…Olu Falae ya karbi naira miliyan dari (N100 million)
20…Fayose ya karbi naira biliyan uku  ( N3 billion)
21…Nenadi Usman ta karbi naira biliyan uku da miliyan Dari biyar.( N3.5 billion)
22…Femi Fani-Kayode ya karbi naira miliyan dari bakwai da arbain (N740 million)
23…Patience Jonathan tace dala miliyan talatin da daya nata ne na ganin likita..($31 million dollars)
24…. Nasan dai kuna da labarin makudan kudaden da tsohuwar ministan man fetur Diezani Alison Madueke tare da yaranta suka kwashe daga asusun gwamnatin tarayya a shekarun baya….
Dukkan wadannan makudan kudaden anyi ruf da ciki da sune a lokacin gwamnatin baya…..

You may also like