Tun bayan da Shugaba Donald Trump, ya sanya hannu kan dokar hana musulmin wasu kasashe bakwai shiga Amurka, Duniya ke ci gaba da sukan matsayinsa da nuna shakku da kuma alamun tambaya.
kafofin yada labarai da dama a duniya sunyi sharhi kan wannan batun kuma abunda suka fi maida hankali akan shi ne yadda wannan matakin da sabuwar gwamnatin Amurka ta ce na yaki da ta’addanci ne bai shafi wasu kasashe da ake ganin su ne tushen hadassawa da kuma taimakawa ayyukan ta’addanci.
Matakin dai na Shugaba Trump ya shafi kasashe bakwai da suka hada (Iran, Irak, Yemen, Somalia, Sudan, Syria da kuma Libya) saidai masu bibiyar al’amuran yau da kulun sunyi nazari sun ga cewa wannan matakin bai shafi kasashen da suka hada da Afganistan , Pakistan da kuma Saudiyya ba wace sanin kowa ne 15 daga cikin kwamadodi 19 da sukayi garkuwa tare da kai harin 11 ga watan Satumba 2001 ‘yan asalin kasar Saudiyya ne.
Wasu dai na ganin cewa wannan babu shaka bai rasa nasaba da manufofin Amurka a wadanan kasashen, a yayin da wasu ke cewa A’A akwai fa kaddarori da shi sabon shugaban Amurka yake dasu a wadanan kasashen.
Da yake amsa tambayoyi daga gidan talabijin na France 24, Khalil Jahchan wani mai sharhi kan al’amuran siyasa kana shugaban cibiyar Arab Center of Washington dake nazari kan harkokin diflomatsiyan Amurka a kasashen Larabawa, ya ce ya kadu matuka akan wannan matakin na Donal Trump wanda bashi da wata alaka da hakikanin barazana da Amurka ke fuskanta akan ayyukan ta’addanci, don saboda a cewarsa wasu kasashe wadanda ‘yan kasarsu suka kai harin ta’addanci har cikin Amurka basa cikin jerin kasashen da wannan matakin ya shafa.
Mista Jahchan ya ce dubi Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa Saudiyya wace ‘yan kasar ne suka kisa harin 11 ga watan Satumba, duka babu su a cikin jerin wadanan kasashen, ga kuma Turkiyya wace ke ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci a ‘yan watannin nan wace har ma Amurka ta gargadi ‘yan kasar dasuyi taka sansan wajen shiga kasar a yanzu.
Hakazalika ma a cewar wasu kafofin yada labaren Amurka wannan kin hadawa da wadanan kasashen ba wai abunda za’a cewa an manta da shi ne ba, Kungiyar (Trump Organization) na da hulda da harkoki sosai a galibin wadanan kasashen duk da cewa Sabon shugaban Amurka din ya ce zai mika ragamar jagorancin wannan kungiyar data shahara wajen saida manya gidaje ga ‘ya ‘yansa biyu domin kaucewa duk wani zargi.
Kanfanin dai na Trump ya mallaki wasu mayan gidaje a kasahen Larabawa da dama ciki kuwa da akwai mayan gidaje na kece alfarma a birnin Satambul na Turkiyya, wadanda a shekara data gabata kawai sun samar mashi da Dalla Miliyan 5 na Amurka, da kuma wani filin wasan Golf a Dubai mai daukeda sunan Trump da kuma wasu kanfanoni biyu a Masar wadanda dai basu aiki a yanzu, sai kuma wasu mayan kanfanoni guda takwas da shugaba Trump din ya mallaka a Saudiyya da suka hada da Otel THC (Jeddah Holtel Manager) wanda aka bayyana a cikin kaddarorin da shugaban mallaka gaban kwamitin hukumar zaben Amurka mai kula da sha’anin kudi FEC.
Wadanan alamomin dama yadda wadanan kasashen da suka hada da Saudiyya wace Sarkin ta Salmane ya tattauna ta wayar tarho da sabon shugaban sukayi gum da bakinsu akan wannan matakin na hana musulmi shiga Amurka ya nuna karara alamun tambaya da kuma shakku dake a zukatan al’umma………..