Ko Me Yasa Buhari Ya Yanke Shawarar Sake Komawa Kan Karagar Mulki?


Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana cewa ya yanke shawarar sake tsayawa takarar Shugaban kasa ne saboda mafi yawan al’ummar Nijeriya sun yaba da irin ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

Shugaban ya yi wannan ikirarin ne a birnin Landon a lokacin da ya sadu da amininsa, Shugaban Cocin Canterbury, Justin Welby inda ya nuna cewa an jima mutane na maganganu game da batun ko zai sake tsayawa takara wanda a kan haka ne, ya fito karara ya bayyana ra’ayin nasa na shiga takarar.

Game da rikicin makiyaya da manoma, Shugaba Buhari ya shaidawa amininsa cewa tsohon Shugaban Libya, Marigayi Mu’ammar Ghaddafi ne ya horas tare da bayar da makamai ga wasu makiyaya wanda baya kifar da mulkinsa, shi ne suka arce kuma suka shigo Nijeriya suna aikata ta’addanci.

Buhari ya nuna cewa a can baya an san makiyaya suna dauke da sanda ne a maimakon yanzu, da ake ganin su da manyan bindigogi inda ya nuna takaicinsa kan yadda shigo da siyasa cikin wannan rikici na makiyaya da manoma wanda rikici ne mai dogon tarihi.

You may also like