
Asalin hoton, Getty Images
Argentina za ta kara da Faransa a wasan karshe a Gasar Cin Kofin Duniya ranar Lahadi da Qatar ke karbar bakunci.
Ko Messi zai dauki Kofin Duniya na farko a tarihi, ko kuwa Mbappe zai lashe na biyu a jere a karawar da za su buga a filin wasa na Lusail.
Messi mai shekara 35, ya lashe Ballon d’Or bakwai da Copa America da sauran kofuna da yawa, amma bai taba daukar na Duniya ba.
Argentina mai Kofin Duniya biyu jumulla, amma rabon ta da shi tun 1986 karkashin jagorancin Diego Maradona.
Wannan karawar za a yi tsakanin ‘yan kwallon Paris St Germain da suke taka leda tare, wato Messi da Kylian Mbappe.
‘Yan wasan biyu na takarar lashe kyautar takalmin zinare a matakin, wanda ke kan gaba a cin kwallaye a Gasar, kowanne yana da biyar-biyar a raga a Qatar.
Yayin da Olivier Giroud na Fransa da dan kwallon Argentina, Julian Alvarez kowanne yana da hur-hudu a raga.
Messi ya ja ragamar Argentina kai wa wasan karshe a Gasar Kofin Duniya a 2014, amma Jamus ta doke su 1-0 a Brazil, bayan karin lokaci, Mario Gotze ne ya ci kwallon.
Argentina ta lashe kofin Duniya guda biyu na farko a gida a 1978, sannan a 1986 a Mexico.
Faransa ma biyu ne da ita, wadda ta fara dauka a gida a 1998, sannan ta lashe a 2018 a Rasha.
Kowacce na fatan daukar na uku jumulla, sai dai Fransa na sa ran daukar na biyu a jere bayan bajintar da Brazil ta yi a 1962 – sai dai Italiya ce ta kafa tarihin cin biyu a jere a 1934 da kuma a 1938.
Asalin hoton, BBC Sport
Karawa tsakanin tawagogin biyu
Gasar Kofin Duniya Asabar 30 ga watan Yunin 2018
- France 4 – 3 Argentina
Wasan ssada zumunta Laraba 11 ga watan Fabrairun 2009
- France 0 – 2 Argentina
Wasan sada zumunta Laraba 7 ga watan Fabrairun 2007
- France 0 – 1 Argentina
Gasar Kofin Duniya Talata 6 ga watan Yunin 1978
- Argentina 2 – 1 France
Gasar Kofin Duniya Talata 15 ga watan Yulin 1930
- Argentina 1 – 0 France
Asalin hoton, BBC Sport
Wasu batuwan da ya kamata ku sani kan wasan
Sun kara sau uku a Gasar Kofin Duniya, inda Argentina ta yi nasara a fafatawar cikin rukuni a 1930 da kuma 1978 – sai dai Faransa ce ta ci Argentina 4-3 a zagayen ziri daya kwale a 2018.
Argentina za ta buga wasan karshe na shida a Gasar Kofin Duniya, Jamus ce kan gaba a yawan kai wa fafatawar karshe mai takwas.
Argentina ta dauki Kofin a 1978 da 1986, sannan aka doke ta a karawar karshe a 1930 da 1990 da kuma 2014.
Watakila Argentina ta zama ta biyu da ta yi rashin nasara a wasan farko a Kofin Duniya, sannan ta lashe Gasar kamar yadda Sifaniya ta yi a 2010.
Haka kuma kila Messi ya zama na uku daga Argentina da zai lashe takalmin zinare, bayan Guillermo Stabile a 1930 da kuma Mario Kempes a 1978.
Faransa ta halarci karawar karshe a Gasar Kofin Duniya karo na hudu.
Faransa na fatan zama ta uku da za ta lashe Kofin Duniya biyu a jere, bayan Italiya a (1934-38) da kuma Brazil (1958-62).