
Asalin hoton, Getty Images
Croatia za ta kara da Morocco a wasan neman mataki na uku ranar Asabar a Gasar Kofin Duniya da ake yi a Qatar.
Morocco ta kawo wannan matakin bayan da ta yi rashin nasara a wajen Faransa a karawar daf da karshe, ita kuwa Croatia ta sha kashi a hannun Argentina.
Kociyan Morocco, Walid Regragui ya ce kasar tana alfari da za ta buga wasa na bakwai a Gasar Kofin Duniya a Qatar, duk da cewar ba ta kai wasan karshe ba.
Ko a yanzu Morocco ta zama ta farko daga Afirka da ta kai daf da karshe a babbar Gasar tamaula da Fifa kan gudanar tun daga 1930.
Morocco da kuma Croatia, wadda ta yi ta biyu a Rasha na fatan kara fuskantar juna a neman mataki na uku a Qatar, bayan da suka tashi ba ci a karawar cikin rukuni.
Sun kara ba ci a rukuni na shida ranar 23 ga watan Nuwamba a filin wasa na Al Bayt, sai dai Regragui na fatan Morocco ta zama ta uku a Qatar.
Watakila shi ne wasa na uku da kyaftin, Luka Modric, mai shekara 37 zai yi wa Croatia, mai taka leda a Real Madrid.
Asalin hoton, Getty Images
Labari kan tawagogin biyu
Regragui ya tabbatar cewar Romain Saiss na jinya, ba zai yi wasan ba, wanda ya saka shi a daf da karshe amma rauni ya hana shi sakat a minti na 20 da fara tamaula.
Croatia za ta yi fafatawar ba tare da Marcelo Brozovic, wanda ya ji rauni a karawar da Argentina ta yi nasara a daf da karshe.
Haka shima mai tsaron bayan Croatia, Josko Gvardiol na jinya ba zai yi wasan ba.
Wasu batutuwan da ya kamata ku sani
Daga wasa 19 da aka buga a baya, ba wanda ta kai bugun fenariri, sai guda daya da ta kai ga karin lokaci a 1986 tsakanin Faransa da Belgium.
Tawaga daga Turai ta yi ta uku a Gasar Kofin Duniya 10 da aka yi a baya tun bayan da Brazil ta yi nasara a kan Italiya a 1978.
Wannan shi ne wasa na biyu a matakin neman na uku da Croatia za ta yi, bayan da ta ci Netherlands 2-1 a 1998.
An zura wa Croatia kwallo uku a karawar da ta yi da Argentina a daf da karshe a Qatar, fiye da wadanda aka zura mata a raga a karawa biyar a 2022.
An kuma kai mata hare-hare har sau 75 fiye da kowacce tawaga a Qatar.
Kwallo biyu ne suka shiga ragar Morocco da Faransa ta yi nasara, bayan da Morocco ta ci gida a wasan da ta yi nasara a kan Canada da ci 2-1 a cikin rukuni.
Za ta zama ta takwas mai wasa biyar da kwallo bai shiga ragarta ba a Gasar Kofin Duniya, bayan bajintar Netherlands (1974), Italy (1990), Brazil (1994), Faransa (1998), Jamus (2002), Italiya (2006) da kuma Sifaniya (2010).
Modric ya buga dukkan wasan Croatia shida a Qatar, mai tsaron raga Peter Shilton (1990) da Dino Zoff (1982) sune kan gaba masu shekara 37 da suka yi karawa bakwai gabaki daya.
Ivan Perisic ya ci kwallo shida a Gasar Kofin Duniya – saura daya ya sha gaban Davor Suker a matakin kan gaba a ci wa Croatia kwallaye a babbar Gasar ta Fifa..