
Asalin hoton, Getty Images
Newcastle United za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan mako na 29 a gasar Premier League ranar Lahadi a St James Park.
Sun tashi 0-0 a Old Trafford a Premier League ranar 16 ga watan Oktoban 2022, sannan United ta ci 2-0 ta lashe Carabao Cup ranar 16 ga watan Fabrairun 2023 a Wembley.
United tana mataki na uku da maki 50 a teburin Premier, ita kuwa Newcastle tana ta biyar mai maki 47, bayan da suka yi karawa 26 kowacce.
Dan kwallon Newcastle, Joelinton zai iya buga wasan, bayan hukuncin dakatarwa, da kyar idan Anthony Gordon zai yi karawar, saboda jinya.
Watakilan Nick Pope da Sven Botman su yi wasan bayan jinya, wadanda ba su buga wa tawagoginsu tamaula ba.
An tabbatar Callum Wilson da Allan Saint-Maximin za su iya buga fafatawar, amma Miguel Almiron na ci gaba da jinya.
Kocin, Manchester United, Erik ten Hag na fatan Marcus Rashford zai iya buga wasan, wanda ya yi jinyar da bai yi wa Ingila karawa biyu ba.
Tawagar Ingila ta je ta ci ta Italiya 2-1, sannan da doke Ukraine 2-0 a Wembley a wasan neman shiga gasar Euro 2024 da Jamus za ta karbi bakunci.
Anthony Martial ya warke, sai dai da kyar idan Marcel Sabitzer da Raphael Varane za su yi wasan, domin basu murmure ba.
Christian Eriksen da Alejandro Garnacho da Tom Heaton ba za su buga wasan ba, sakamakon jinya.
Karawa tsakanin kungiyoyin biyu:
Asalin hoton, Getty Images
Akwai karin bayanai……………