Ko ya dace India ta soke gwamnonin jihohi?



Hoton jagoran jam'iyya da gwamna

A makon da ya gabata ne Kotun Ƙolin India ta ce gwamnonin ƙasar za su iya lalata dumukuraɗiyyar ƙasar idan har abubuwan da suke yi suka haifar da faɗuwar gwamnatin wata jiha.

Kotun na magana ne a kan gwamnan jihar Maharashtra da ke yammacin ƙasar, wanda ya nemi a kaɗa wata ƙuri’ar ƙauna mai ka-ce-na-ce a majalisar dokokin jihar tasa a shekarar da ta wuce, wanda hakan ya kai ga faɗuwar gwamnatin jihar a lokacin.

Jam’iyyar Shiv Sena waddaa ita ce ta gwamna Uddhav Thackeray, ta kasance mafi girma a haɗakar gwamnatin jihar ta Maharashtra.

To amma wasu da suka yi tawaye sun raba jam’iyyar suka yi sabuwar haɗaka da jam’iyyar Firaminista Narendra Modi wato Bharatiya Janata Party (BJP), wadda ke mulkin ƙasar ta Indiya.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like