Ko me zai faru ba za mu bar garin Mosul ba


 

 

Shugaban Kungiyar ta’adda ta Daesh Abubakar Albagdadi ya fitar da falfan sauti inda ya ce, ko ma me zai faru sai dai ya faru amma ba za su fita daga garin Mosul ba.

Labaran da jaridar Independent ta Birtaniya ta fitar a ranar Larabar nan na cewa, shugaban ‘yan ta’addar da ke boye a Mosul ya rusa shirin da ya yi na watanni 8.

A labaran da Rueters ta fitar amma kuma ba a tabbatar da gaskiyar maganganun na Albagdadi ba na mintuna 31 an ji shi yana cewa, ko ma me zai faru sai dai ya faru amma ba za su fita daga garin Mosul ba.

A maganganun nasa ya kuma ce, za s yi nasarar wannan yaki da ake yi a Mosul.

Shugaban na ‘yan ta’addar ya kuma bukaci mmabobinsa da su kara yawaita kai hare-haren kunar bakin wake.

A maganganun ya yi kira da a kai wa Saudiyya kafirar kasa hari.

Tun shekarar 2014 Daesh ta kwace Mosul inda Bagdadi ya ayyana Halifanci a garin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like