Koda Wani Abu Ya Faru, Osinbajo Bazai Maye Gurbin Buhari Ba – Dattawan ArewaMajalisar Dattawan Arewa ta bayyana cewa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ba shi ya kamata ya gaji kujerar shugaban kasa ba a 2019 idan wani abu ya faru da Buhari.


Shugaba Buhari dai yanzu haka ya na birnin London a kasar Burtaniya, inda ya je ganin likitocin shi.

Shugaban majalisar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya jaddada cewa mulkin Nijeriya zai kasance ne a Arewa ko da ace shugaban kasa Buhari ya fasa tsayawa takara a 2019.

Ya ce duk da cewa dokar kasa ta tanadar da cewa Osinbanjo shi zai karasa mulkin da suka fara tare da Buhari idan wani abun ya faru, amma ba zai iya yin takara ba a 2019.

A ra’ayin su, dole ne jam’iyyar APC ta tsayar da wani dan takarar shugaban kasa daga Arewa idan za ta bi ka’idar siyasar karba karba.

Ya ce babu wanda ya san lokacin da Buhari zai ji saukin da zai iya ci gaba da gudanar da mulkin kasar, kuma babu wanda ya sani ko ta Allah za ta kasance, a don haka suna tsammanin za a yi wa Arewa adalci idan wani abu ya faru

You may also like