Ajantina ne ta yi nasara a gasar cin Kofin Duniya na 2022 a karo na uku bayan ta doge Faransa a bugun fenareti a gasa Kofin Duniya a Qatar.
Gonzalo Montiel shi ne ya ci kwallon da ta bai wa kasar ta yankin kudancin Amurka nasarar 4-3, bayan kunnen doki na 3-3 a wasan da ya kai su ga karin lokaci na minti 30.
Lionel Messi ya zura ƙwallaye sau biyu, da Angel di Maria ya ci wa Ajantina ƙwalo ɗaya, yayin da ɗan wasan Faransa, Kylian Mbappe ya zama ɗan wasan farko tun bayan Geoff Hurst a 1966 da ya ci ƙwallaye uku a wasan ƙarshe na kofin duniya.
Ajantina ta sun rike kambunsu na cin kofin duniyar har sau uku, da Messi a matsayin dan wasan mafi iya buga kwallon ƙafa,a filin wasa na Lusail.
Ga yadda wannan wasa dake ci ke da tarihi, da za mu kawo muku su a cikin hotuna mafi kyau, a wani wasa da ya kayatar.
Asalin hoton, Getty Images
Bayan buga wasannin 63, a kasa da wata guda, gasar cin kofin duniya na 2022 ya zo ƙarshe, inda Ajantina zata kara da Fransa a filin wasa na Lusail. Farawa da bikin rufe gasar, hakn na nufin fara wannan biki…..
Asalin hoton, Getty Images
Ajantina ta fara wasan da karfinta, hakan yasa su ka sami bugun da kai sai mai tsaron raga, a minti na 23 bayan da Ousmane Dembele ya yi wa Angel di Maria ƙeta. hakan ya tuzura Messi, ya sa kasar a gaban a wasan
Asalin hoton, Getty Images
Ajantina ta sa ke amfani da damar da ta ke da shi a zagen waan na Farko, inda Di Maria ya yi amfani da wata kora da su ka kai, ya buga kwallon ta wuce mai tsaron ragar Hugo Lloris. A wannan gaɓa kasar dake Nahiyar Kudancin Amuraka, ta , ta fara jin kanshin nasara cin kofin………
Asalin hoton, Getty Images
Bayan gazawar su kai hari da’ira ta 18 a cikin miniti na 67, Kylian Mbappe ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai taron gida, bayan da Nicolas Otamendi ya yiwa Randal Kolo Muani ƙeta.
Asalin hoton, Getty Images
Murna ta dawo bayan da Mbappe ya doka kwallon d ata wuce Emi Martinez, da hakan yasa kasashen biyu kunne doki 2-2. Wanda sakan 97 ne tsakanin kwallo ta farko da ta biyun da ya ci
Asalin hoton, Getty Images
Wasan ya kai ga kwarin lokacin bayan cikiar mitin 90, in da Messi ya sake zurawa Ajantina Kwallon da ta wuce Lloris ya tare kwallon Lautaro Martinez. Jules Kounde ya yi kokarin tare kwallon amma bai yi nasara ba.
Asalin hoton, Getty Images
Faransa da Mbappe bas u yarda na cin ye su ba, wani hari kwallon da aka kai dan wasan Ajantina ya tare da hannun, wanda hakan ya baiwa dan wasan kungiyar kwallo na PSG mayar da wasan 3 – 3
Asalin hoton, Getty Images
… hakan ya sa a tsawon shekaru 56, ya zama dan wasan ana farko a ajin maza, a ya zura kwallo har uku a wasan karshe na gasar kofin duniya. bayan bugun daga kai sai mai tsaron raga a tsawon minti 120,
Asalin hoton, Getty Images
Mbappe da Messi ne suka fara bugun daga kai sai mai tsaron raga, dukkansu kuma su yi nasara zura kwallon. Sai dai tsaron ragar kungiyar Aston Villa Emiliano Martinez ya tare kwallon dan wasan Faransa Kingsley Coman
Asalin hoton, Getty Images
An bar Faransa a baya, bayan da mai bugunsu na uku Aurelien Tchouameni, ya bara musu da kwallo
Asalin hoton, Getty Images
Gonzalo Montiel, wanda aka ya shigo wasan a minti na 90, bayan ya canjin ɗan wasan baya, ya buda ya yi nasarar zura kwallo da ya mayar da bugun daga kai sai mai tsaron raga ya ko ma 4-2
Asalin hoton, Getty Images
Montiel ya rufe fuskarsa da rigarsa bayan da ya zura kwallon da ya zura, kwallon da ta basu nasarar lashe bungun daga kai sai mai tsaron gida, kafin yan kasarsa su rungume shi cikkin murna.
Asalin hoton, Getty Images
An ayyana Messi a matsayin dan wasan Gasar wadan aka ba shi lambar talaklmin zinare. Kyautar zinare daya ya sa idonsa akai……..
Asalin hoton, Getty Images
Wannan shi ne karo na uku da Ajantina ta ta dauki kofin duniya, bayan daukar kofin a shekarar, 1978 da 1986. Hakan na zuwa ne shekaru biyu bayan mutuwar Diego Maradona, wanda ya yi nasara daukar kofin sau biyu.
Asalin hoton, Getty Images
Messi ya kasance a sama duniya, a ranar Lahadi