Kokarin magance rikicin Niger Delta


Jami’an tsaro sun kama wasu mutane guda tara da ake zargi da bai wa ‘yan tawaye wasu sinadarai da ake hada bama-bamai da su a yankin Niger Delta.

 

 

Da yake magana tare da wakillan wani kanfani na yankin Niger Delta kan wannan batu, Janar Mohammed Monguno da ke a matsayin mai bada shawara kan harkokin tsaro a Tarayyar ta Najeriya, ya ce wani bincike mai zurfi da aka aiwatar, ya nunar cewa an sace akalla kg 9000 na sinadaran hada ababe masu fashewa da kuma wasu ababen masu fashewa 16.450 inda aka sayar da su ta hanyar da ba ta gaskiya ba.

Janar din ya ce daga cikin wadanda aka kama akwai mai kula da runfar ajiye kayayakin na wani kanfani, da wani mai taimaka masa sannan da jami’an tsaro guda biyar. Kuma binciken ya nunar cewa, ababen da ake amfani da su wajen kai hare-haren, ana hadasu ne ta hanyar sinadirai na Nitrate da ake amfani da su wajen yin takin zamani.

You may also like