Kokarin sasanta Armeniya da Azerbaijan | Labarai | DWMinistar harkokin wajen Faransan Catherine Colonna ce ta yi wannan kira, yayin wani taron manema labarai a Yerevan babban birnin kasar Armeniya. Ziyarar tata a Armeniya na zuwa ne jim kadan bayan tattaunawarta da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev a fadarsa da ke birnin Baku, inda ta ce ya kamata a girmama martabar yankunan Armeniyan. A nasa bangaren takwaranta ministan harkokin waje na Armeniyan Ararat Mirzoyan ya bayana cewa, tilas a dawo da ‘yancin zirga-zirga a yankin. Azerbaijan dai ta sanya shingen ne a Lahadin karshen mako, matakin kuma da makwabciyar kasa Armeniya da ke zaman abokiyar hamayyarta ta tir da shi. Kassashen biyu da ke makwabtaka da juna, sun kwashe tsawon lokacin suna rikici a kan yankin nan na Nagorno-Karabakh da ke kan iyakokinsu.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like