Komiti mai bawa shugaban tarayyar Nigeria shawara kan yaki da cin hanci da rashawa ta bukaci a dakatar da alkalan da ake tuhuma da cin hanci da rashawa daga aiki.
Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta bayyana cewa komitin da ke bawa shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci da rashawa ya bukaci a dakatar da alkalan da ake tuhuma a hukumar DSS daga aiki.
Shugaban komitin Professor Bolaji Owasanoye ya yi wannan kiran ne a jiya a lokacinda yake zantawa da yan jarida a Abuja, ya kuma kara da cewa bai kamata alkalan da ake tuhumar a gaban wata kotu ya kasance suma suna ci gaba da sauraron wasu kararraki a kotunansu ba.
Professor Bolaji ya kara da cewa a duk duniya idan ana tuhuamar alkali a wata kotu to zai ajiye aikinsa ne ya ci gaba da kare kansa, har zuwa lokacinda za’a wanke shi ko kuma a kama shi da laifi. Ya kuma kara da cewa duk alkalin da ya ci hanci ko ya karbi rashawa to aikata laifin babban laifi ga bil’adama, sannan ya zargi wadanda suke zargin hukumar DSS da cewa basu yi hangen nesa a kan lamarin ba, don duk alkalin da ya lalata ce ya ci mutuncin kasarsa ne.
Professor Bolaji Owasanoye ya ce akwai wasu gwamnoni a baya basu ci zabe be amma wasu alkalai suka hukunta masu da cin zaben, don haka akwai bukatar a tsarkake ma’aikatar sharia daga irin wadan nan baragurbi inji shi.
Fiye da alkalai 10 ne daga johohi daban daban suke amsa tambayoyi a hukumar DSS ta yansandan ciki kafin a gurfanar da su a gaban kotu a Abuja.