A jihar Florida ta Amurka an kona wani masallacin Juma’a wanda matashin da ya kai hari a gidan rawan ‘yan luwadi a ranar 12 ga watan Yuni Umar Mateen ya ke zuwa.
Babu wani da ya mutu ko jikkata sakamakon kona Masallacin wanda babu kowa a ciki a lokacinda aka kai harin amma kuma an yi asara mai yawa.
Jama’ar da suke kusa da Cibiyar Addinin Musulunci a garin Pierce ne suka hango wuta na ci a Masallacin.
An bayyana cewa, za a yada hotunan da aka samu na mutumin da ya sanya wutar domin jama’a su taimaka wajen kamo shi.
An bayyana cewa, wannan Masallaci da aka kona ne Umar Mateen da ya kai hari da daddare a gidan ‘yan luwadi yana zuwa.
Umar Mateen ya kashe mutane 49 a harin na bindiga da ya kai a gidan ‘yan luwadin da ke Orlando. Kuma an kashe shi a rangamar da suka yi da ‘yan sanda.