Koriya ta Arewa: Sake gwajin makamai | Labarai | DWWannan sabon gwajin makaman dai, na zuwa ne gabanin ziyarar da mataimakiyar shugabar Amirka Kamala Harris za ta kai makwabaciyar Koriya ta Arewan kana abokiyar tagwaitakarta da kuma takun sakarta Koriya ta Kudu. Rundunar sojojin Koriya ta Kudun ta bayyana cewa, ta gano makamai masu linzami da ba sa cin dogon zango guda biyu da aka harba daga fadar Pyongyang. Rahotanni sun nunar da cewa an harba makami na biyu, mintuna 10 bayan harba na farko. You may also like