
Asalin hoton, Reuters
Kim Ju-ae na kallon faretin tare da mahaifinta
Koriya Ta Arewa ta yi bajakolin nuna makamanta mafiya girma masu cin dogon zango na ƙasa da ƙasa, adadin da ya janyo masu hasashe ke ganin ƙalubale ne ga tsarin tsaron Amurka.
Kimanin manyan makamai 12 aka nuna a ranar Laraba a wani faretin soji.
An ga shugaba Kim Jong-un da ‘yarsa a gefensa lokacin da ake faretin a cikin dare.
Bayyanar da ta yi a yayin wannan fareti, ya janyo ce-ce-ku-ce kan cewa kila ita ce za ta gaje a nan gaba.
Yawan makaman da aka nuna ya janyo damuwa ƙwarai.
Masu hasashe sun ce irin adadin makaman da aka fitar – waɗanda aka ce za su iya kaiwa har cikin ƙwaryar ƙasar Amurka – za su iya zama barazana ga tsarin tsaron nukiliyar Amurka, idan kowanne ɗaya na ɗauke da wasu ƙananan makamai a cikinsa.
Kafafen yaɗa labaran Koriya ta Arewa ba su yi ƙarin bayani kan makaman ba – amma nuna irin waɗannan makaman kan “haifar da rashin tabbas ta fannin yaƙi”.
Wasu hotuna da kafafen yaɗa labarai na Koriya Ta Kudu suka wallafa a ranar Alhamis sun nuna makamai sama da 12 ana tura su ta tsakiyar dandalin Pyongyang sojoji na raka su a ƙafa.
Asalin hoton, Reuters
An ƙaddamar da makaman yayin faretin
Masu hasashe a ƙasar sun ce an gabatar da wani sabon makami na musamman, da za a sanya masa wata na’ura da za ta rika taimakawa ya kai yadda ake so, sama da wanda ake zuba wa fetur.
Amma duk da haka, ba a taɓa yin nasarar gwada makamin mai amfani da wannan na’urar ba ta musamman a lokacin Kim.
“Wannan dai daya ne daga cikin manyan baje-kolin da Koriya Ta Arewa ta yi,” in ji Panda, wata kwararriya kan harkokin nukiliya a ƙungiyar Carnegie Endowment for International Peace.
“Muna sa ran ganin jirgin sama na farko da zai yi gwajin wannan makami nan da watanni masu zuwa,” ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa faɗaɗa rumbun makaman masu cin dogon zango da Koriya ta yi na nufin, wani gagrumin shiri na ƙalubale ga Amurka a wannan rikici, kuma zai iya zama abu mawuyaci ga Amurka ta gano sannan ta lalata duka ma’ajiyar makaman na Koriya Ta Arewan.
Bayyanar da Ju-ae ta yi – mai kimanin shekara 10 – ya zama wani abin magana a wajen masu bibiyar lamura.
Asalin hoton, Reuters
Kim Ju-ae da mahaifnta Kim Jong-un tare da mahaifiyarta Ri Sol Ju
Wani hoto da kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta wallafa ya nuna ta a tsakiyar wani hoto da aka ɗauka gabanin fara faretin sojin, inda take zaune tsakanin Mista Kim da matarsa Ri Sol Ju, wani wurin zama da mahaifinta ke ba ta a mafi yawan lokuta.
Su ukun suna murmushi a hoton kuma manyan kwamandojin sojin ƙasar na tsaye a bayansu.
An rawaito cewa Kim Jong-un na da yara aƙalla uku, ciki har da babban ɗansa namiji da ƙaramar ‘yarsa mace. An kuma yi amannar Ju-ae ce ‘yarsa ta biyu.
A watan Nuwamban da ya gabata ne aka fara ganin ta a bainar jama’a, yayin da mahaifinta ya ɗauke ta zuwa ƙaddamar da makamai masu cin dogon zango.
Yayin da ake kallon maye gurbin Kim a matsayin gagarumin abu, yanzu ya yi wuri a ce ga wanda zai gaje shi, kamar yadda Mista Williams ya shaida wa BBC.