Rundunar ‘yan sandan jahar Kogi ta gurfanar da babban dan tsohon gwamnan jahar Kogi marigayi Abubakar Mohammad Audu a kan zargin laifin fashi da makami.
Bayyanar Mohammad kotu a matsayin wanda ake tuhuma ya yi matukar baiwa mutane mamaki.
An gurfanar da Mohammad ne a kotun majistare da ke Lokoja a jiya Alhamis bayan da aka kama shi a ranar Laraba.
Jami’an sashen yaki da fashi da makami na rundunar ‘yan sandan sun gayyaci Mohammad zuwa ofishinsu ne daga bisani suka tsare shi.
Banda laifin fashin, kotu na kuma tuhumar shi da hada kai a aikata laifi da zalunci da yunkurin kisa wadanda suka sabawa sashe na 97 (1), 248, 327, 298 da na 229 kundin dokar kasa.
Alkalin kotun mai shari’a Alhasan Husaini ya bayarda belin Mohammada ya kuma daga sauraran karar zuwa ranar 29 ga watan nan.