Kotu ta bada belin Ɗanbilki Kwamanda


An gurfanar da Abdulmajid Danbilki kwamanda, a gaban kotu wani fitaccen magoyin bayan shugaban ƙasa Muhammad Buhari.

Kwamanda ya gurfana gaban mai sharia Kabiru Tareka  na kotun majistire dake yankin Nomansland a Kano.

Ƴansanda ne suka kama Kwamanda a ranar Litinin bayan da wasu mutane uku ciki har da mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen yaɗa labarai, Sha’aban Ibrahim Sharada suka shigar da korafi a kansa.

Alkalin kotun mai shari’a Kabiru Tareka ya bada belinsa kan kuɗi naira miliyan ₦2,000,000 da kuma wasu mutane biyu da za su tsaya masa.

Ɗaya daga cikin mutanen da za su tsaya masa dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnati dake matakin albashi na 14 ko fiye da haka yayin da ɗayan kuma dole ya zama mazaunin Kano dake da kadara da darajarta ta kai miliyan ₦50.

You may also like