Wata babbar kotu dake birnin tarayya Abuja ta bada belin sanata Dino Melaye kan kudi naira ₦100,000.
Gwamanatin tarayya ce ta gurfanar da Melaye a gaban kotu tana zarginsa da aikata laifuka biyu da suka hada da kalawa, Edward David, sharri shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kogi kan yinkurin aikata kisa.
Melaye ya zargi Edward da hannu a yunkurin hallaka shi a wani hari da yan bindiga suka kai masa a shekarar da ta wuce.
A zaman kotun na yau Melaye ya ki amincewa da dukkanin tuhume-tuhumen da ake yi masa.ya yin da Magaji Labaran lauyan gwamnatin tarayya ya nemi kotun da da ta cigaba da sauraron shari’a cikin kwanaki biyu masu zuwa.
A na sa bangaren, babban lauya Ricky Tarfa,dake kare Melaye ya nemi kotu da ta bada belinsa. Ya kuma soki lamirin lauyan gwamanati kan adawar da ya nuna na bada belin.
Bayan sauraron lauyoyin biyu, mai shari’a,Olasumbo Gudluck ya bada belin sanatan ya kuma nemi ya kawo mutane biyu ma’aikatan gwamnati masu matakin albashi na 14 da za su tsaya masa.