Kotu ta bada belin Jang


Wata babbar kotu dake Jos ta bada belin tsohon gwamnan jihar,Joshua Dariye kan kudi miliyan ₦100.

Mai shari’a, Daniel Longji Babbar kotu ta biyar ya bawa Jang umarnin kawo mutane biyu da za su tsaya masa daya daga ciki dole ya kasance basaranke gargajiya dake zaunea hurumin kotun.

Kotun ta kuma umarci hukumar yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFFC da ta mika mata fasfon tafiye-tafiye na tsohon gwamnan.

Jang na fuskantar tuhume-tuhume 12 da suka hada da aikata cin hanci da rashawa da kuma barnatar da kudade da yawansu ya kai biliyan ₦6.3 gab da zai sauka daga mulki a shekarar 2015.

You may also like