Wata kotun Majestiret da ke da zama a garin Ikeja ta jihar Legas ta ba da Belin wata mai sana’ar dinki mai suna Rita Ogbuenyi ‘yar shekaru 28 da ake tuhumarta da laifin buga wa mijinta tabarya a kai.
An bayyana wa kotun cewa wadda ake tuhuma tare da mijinta suna zaune ne a gida mai lamba 18, a unguwar Diamond Estate da ke Ikeja wanda a yanzu haka ake tuhumarta da laifuka biyu da suka hada da hari da kuma ta da hankali.
Wani jami’in dan sanda mai suna Sajan Christopher John ya ce ana tuhumarta ne da laifi rada wa mijinta mai suna Mista Henshawell Ogbuenyi tabarya a kai wanda ya yi sanadiyyar ji masa mummunar rauni.
Jami’in dan sandan ya cigaba da cewa, “wanda ake tuhuma ta aikata hakan ne ga mijinta saboda ya ce mata kar ta fita da kawayenta.”
Ya ce Laifin ya saba sashen doka ta 172 da kuma 166 na laifin ta’addanci a tsarin doka ta jihar Legas na 2015.
Kamfanin dillancin labarai NAN, ta ruwaito cewa sashe na 1 zuwa na biyu ya bayyana akwai hukuncin zaman gidan kaso na shekara 3 ga wanda ya aikita irin wannan laifi, inda a sashe na 166 ya samar da hukuncin daurin wata uku ko biyan taran 45,000 na saba dokar zaman lafiya.
Wadda ake tuhuma dai ta karyata tuhumar da ake yi mata.
A na ta bangaren, mai shari’a Misis M. I. Dan-Oni ta ba da belin wadda ake zargi akan naira 100, 000 inda ta ce hakan zai tabbatar da cewa ita mai biyan haraji ne.
Daga karshe mai shari’ar ta dage sauraron shari’ar har sai ranar 27 ga wannan wata da mu ke ciki ta Maris.