Kotu Ta Bada Belin Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido


Sule_Lamido

Bayan shafe kwanaki huɗu a tsare, kotu ta bada belin tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido batare da ta gindaya wasu sharuɗa ba.

Mai gabatar da ƙara Ikenna Ekpunobi ya soki lamirin bada belin, inda yace Lamido zai iya kawo cikas ga zaman lafiya a jihar. Sai dai  kuma alƙalin kotun mai shari’a Muhammad Lamin yaƙi yarda da iƙirarin da lauyan yayi.

Mai shari’a Lamin ya kuma yi watsi da rahoton da ƴansanda suka gabatar, dake alaƙanta tsohon gwamnan da hargitsin da magoya bayansa suka gudanar.

Lauyan dake kare Sule Lamido Felix John, yace mutumin da yake karewa bashi da laifi har sai an tabbatar da tuhumar da ake masa.Yaƙara da cewa a matsayinsa na tsohon gwamna Lamido bazai tsallake beli ba.

Alƙalin yace laifin da ake zargi Lamido dashi, laifine daza a iya bada belinsa akai.

“Babu wata hujja a gaban kotu dake nuni da cewa mutumin da ake zargi zai tsallake beli,da kuma cewa zai kawo tarnaƙi ga zaman lafiyar jihar”yace

Da safiyar ranar Lahadin da ta gabata ne ƴansanda suka kama Sule Lamido a gidansa dake Ƙano, bayan da gwamnatin jihar Jigawa tayi ƙorafin cewa yana kalaman tunzura al’ummar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like