Babbar kotun tarayya dake zamanta a Maitama,Abuja ta bada belin tsohon gwamnan jihar jigawa Saminu Ibrahim Turaki.
Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC, ce ta kama tsohon gwamnan a Abuja lokacin da yake halartar bikin taron kaddamar da littafi.
Da yake bada belin, mai shari’a Yusif Halilu ya umarci Turaki da ya mika takardunsa na tafiye-tafiye ga magatakardan kotun.
Kotun ta kuma yi umarni da ya gabatar da mutane guda biyu da zasu tsaya masa, mazaunan Abuja da suke da aikin yi.
A karshe mai shari’a Halilu ya umarci Turaki da yakai kansa Ofishin hukumar EFCC a duk mako biyu domin yasa hannu a rijista da za a bude masa yau, har sai ranar da zai gurfana gaban kotun tarayya dake Jigawa, lokacin da kotun zata dawo hutun shekara a watan Satumba.