Kotu ta bada belin Tsohon Shugaban Hafsan sojojin ruwa kan Naira Milliyan 100.


Kotu Ta Bada Belin Tsohon Shugaban Hafsan Sojojin Ruwa Da Sauran Wasu Mutane Biyu Kan Naira Milyan Dari
Kotu ta bada belin tsohon shugaban hafsan sojin ruwa, Usman O. Jibrin da sauran wasu mutane biyu kan naira milyan 100 bisa zargin da ake yi musu na yin babakere da naira milyan 600.
Mai shari’a AS Umar na Babban Kotun birnin tarayyar Abuja ne ya bada belin tsohon shugaban hafsan sojin ruwan da wasu mutune biyu kan laifin da Hukumar EFCC ta gurfana da su.
Sauran biyu sune Rear Admiral Bala Mshelia (mai murabus) da Rear Admiral Shehu Ahmadu (mai murabus)
Hukumar ta EFCC ta gurfanar da su ne a jiya Talata.

You may also like