Kotu ta bada umarnin a yi wa wani barawon wayar hannu bulala 6


Wata Kotun Yanki Mai Daraja Ta Daya dake Karmo, Abuja ta yi umarnin da a yiwa wani, Abdulrahman Sally, bulala shida kan satar wayar hannu.

Sally wanda ke zaune a Utako a Abuja ya amsa dukkanin tuhuma biyu da ake masa ta hada kai da kuma aikata sata.

Alkalin kotun, Alhaji Abubakar Sadiq wanda ya bada umarnin bayan da Sally ya amince da aikata laifin ya ce kotu baza ta yi masa sassauci ba anan gaba idan har ya sake bayyana a gabanta.

Mai gabatar da kara Zanna Dalhatu, ya shedawa kotun cewa wata mata ce mai suna Eugene Dauda dake zaune yankin daya da Sally ta kai rahoton faruwar lamarin a ofishin yan sanda dake Utako ranar 28 ga watan Maris.

Mai gabatar da karar ya ce mutumin da aka yankewa hukuncin tare da wani mutum da ya tsere, sun kwacewa matar dake kara wayarta kirar Tecno wacce darajarta ta kai ₦30,000.

Dalhatu ya ce mutumin da ake nema ya tsere da wayar amma Sally ya shiga hannu da taimakon mutanen da suke wucewa.

Lokacin da yan sanda suke masa tambayoyi ya amince da aikata laifin.

You may also like