Kotu Ta Bayarda Umarnin a Daskarar da Asusun Gwamnatin Jahar Imo


 

Wata kotun daukaka kara da ke zama a babban birnin jahar Imo, Owerri ta bayarda umarnin a daskarar da duk wani asusu mallakar gwamnatin jahar Imo.

Kotun ta bayarda umarnin a yi amfani da kudaden da ke asusunan wajen biyan bashin naira biliyan daya da kamfanin kwangila na E.F Network da wani Mr Gideon Egbuchulam ke bin gwamnatin.

Alkali G. Mbaba ya yanke wannan hukunci ne bayan da gwamnatin ta Imo tare da ma’aikatar man fetur da muhalli ta jahar suka daukaka karar a bisa hukuncin farko da alkali Maryann Anenih ta babbar kotun Abuja ta zartar.

Gwamnatin ta roki kotun ta watsar da hukuncin farko da aka yanke wanda ya goyi bayan kamfanin da Mr Egbuchulam.

Izuwa lokacin rubuta wannan rahoto, babu wani jami’in gwamnatin da ya tofa albarkacin bakinsa game da wannan hukunci


Like it? Share with your friends!

0

You may also like