Kotu Ta Dakatar Da Gwamna El-Rufai Daga Sauke Dagatai Da Masu Unguwanni


Wata babbar kotu dake garin kafancan na jihar kaduna ta dakatar da hukuncin da gwamnatin kaduna ta dauka na sauke dagatai da wasu hakimai wanda yawan su yakai 4000  dake garin. 
A kwanakin da suka gabata ne dai gwamnatin ta jihar kaduna ta fitar da sanarwa sauke Hakimai da dakatai guda 4000 dake fadin jihar kaduna da kewaye. 
A cewar sa, Kwamishinan kananan hukumomi na jihar kaduna Jafaru Sani Yace an dauki matakim sauke dagatan ne saboda matsalar tattalin arziki da matsi da jihar take fuskanta. 
Za’aci gaba da sauraren karar a ranar 29 ga watan da muke ciki wato yuni. 

You may also like