Kotu ta Dakatar Da Taron Gangamin Jam’iyyar PDPBabbar kotun Tarayya a karkashin alkali Okon Abang ya umarci Jam’iyyar PDP data dakatar da taron gangamin data shirya yi a ranar laraba 17/08/2016 a garin Port Harcourt na jihar Rivers.

Hakan ya biyo bayan takaddamar datake cikin Jam’iyyar na cewa Waye halattaccen shugaban Jam’iyyar na kasa a tsakanin Sen.  Ali Modu sherif da kuma Sen. Ahmad Makarfi.

A baya bayannan ne kotun a karkashin judge Abang ta Dakatar da Sen. Ahmad Makarfi da ikirarin da yake na cewar shine Shugaban Jam’iyyar inda bai yadda da hukuncin ba ya kara daukaka kara,  wanda hakan ya kara bashi dama ta kasancewa akan kujerar Shugabancin.

Sen. Ali modu sheriff yace abu ne  mara yiwuwa ayi irin wannan taro ba tare da sanin sa ba wanda hakan nada alaka da dakatar da taron.

You may also like