Kotu Ta Damka Wasu Gidajen Patience Jonathan Ga Gwamnati


Wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta damkawa gwamnatin tarayya wasu gidaje guda biyu mallakar Uwargidan Tsohon Shugaban Kasa, Patience Jonathan.

Rahotanni sun nuna cewa dukkanin gidajen guda biyu suna cikin Babban birnin tarayya Abuja ne wadanda aka mallake shi da sunan gidauniyar Ariwabai Aruera Reachout wadda Patience Jonathan ta kafa a zamanin mulkinsu.

You may also like