Kotu ta daure wani magidanci da ya shekara 7 yana kwana da ‘yar sa a Jihar Kano


Kotu a jihar Kano ta daure wani magidanci mai suna Ibrahim Mohammed saboda kama shi da laifin kwana da ‘yar cikinsa da yake yi.

Ibrahim Mohammed wanda mazaunin Hausawa Quarters ne jihar Kano ya shekara 7 yana kwana da ‘yar ta sa.

Ya fara haka ne tun bayan rasuwar uwarta.

Ita yarinyar ne da kanta ta kai karar uban kotu bayan ta gaji da abin da ubanta ya ke yi mata.

Kotu ta daure Ibrahim Mohammed zuwa lokacin da za ta yanke hukunci akan haka.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like