Kotu ta goyi bayan majalisar dattawa kan kin amincewa da Magu a matsayin shugaban EFCC


Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta ce majalisar dattawa bata saba doka ba lokacin da ta yi watsi da sunan Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati EFCC.

A cewar mai shari’a  JT Tsoho, ya ce majalisar dattawa ba ƴar amshin shata bace kuma tayi haka ne domin bin dokar da ta kafa hukumar EFCC lokacin da ta tantance kuma ta yi watsi da sunan Magu.

An sanarwa da ƴan jaridu hukuncin kotun a ranar Alhamis ya yin wani taron manema labarai.

Sau biyu majalisar dattawa tana ƙin amincewa da sunan Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC amma tun daga wancan lokaci har ya zuwa yanzu ya cigaba da zama a matsayin shugaban riƙo na hukumar.

You may also like