Kotu ta hana Ganduje sayar da asibitiKotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga sayar da asibitin yara da kuma haihuwa dake unguwar Yan Awaki a cikin babban birnin jihar.

Mai sharia Maryam Sabo ta babbar kotun jiha mai lamba 16 dake Miller Road ce ta bayar da umarnin kan karar da al’ummar unguwar suka kai gaban ta.

Salisu Ibrahim Yan Awaki shi ne ya shigar da karar amadadin wasu mazauna unguwar su 113.

Lauyan mutanen yan Awaki Barista Badamasi Sulaiman Gandu ya roki kotun da ta dakatar da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da Antoni Janar na jihar da kuma karamar hukumar Birni da Kewaye daga shirin su na sayar da asibitin.

Mai shariar ta amince da bukatar mutanen unguwar inda ta bukaci mutanen da ake kara da su dakata har sai ranar da za ta sake sauraron karar.


Previous articleNigerian Airforce decorates 51 senior officers to boost security
Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like