
Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a India ta yanke wa wani malamin addinin Hindu hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda yi wa ɗaya daga cikin mabiyansa fyaɗe.
An samu mutumin mai suna Asram da laifin cin zarafin matar sau da dama tsakanin shekarun 2001 da 2006, a wani wurin bauta da ke jihar Gujarat.
Dama dai yanzu haka mutumin mai shekara 81 na ƙarƙashin wani hukuncin ɗaurin na rai-da-rai bayan samun shi da laifin yi wa yarinya ƴar shekara 16 fyaɗe a shekarar 2018.
Lauyansa ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun.
Asaram, wanda ya yi suna kan koyar da ‘yoga’ na da ɗaruruwan miliyoyin mabiya a faɗin duniya.
Hukumomi a jihar ta Gujirat sun tsaurara tsaro gabanin hukuncin kotun na ranar Talata domin gudun tashin-tashina daga mabiya malamin.
Sauran mutum shida waɗanda ake zargi a lamarin an wanke su saboda rashin isasshiyar hujja.
Kotu ta kuma yanke hukuncin tara na kuɗin India rupee 23,000, sannan ta buƙace shi ya biya matar da ya ci zarafi diyyar rupee 50,000.
A shekarar 2013 ma an yanke wa ɗan Asram, mai suna Narayan Sai, hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda laifin yi wa ƙanwar matar fyaɗe.
An kama Asram ne a 2013 bayan wasu iyaye mabiyansa sun shigar da shi ƙara bisa zargin shi da yi wa ƴaƴansu fyaɗe.
Ƴan sanda sun ce Asram ya aikata fyaɗen ne bayan ya kira matar zuwa wurin ibadarsa da ke birnin Jodhpur da nufin yi mata magani.
Sun ce ya kuma yi barazanar kashe wasu daga cikin iyalanta matuƙar ta fallasa lamarin.
Haka nan an yanke wa wasu mataimakan malamin hukuncin ɗaurin shekara 20 saboda rawar da suka taka wurin aikata laifin.