Kotu TA Karbe Biliyan 61 Daga Hannun Tsohuwar Ministan Man Fetur Diezani MaduekeBabban Kotun Tarayya dake Lagos ta bada umarnin karbe dalar Amurka miliyan 153.3 kwatankwacin sama da naira biliyan 61 daga hannun tsohuwar Ministar man fetur ta kasa, Diezani Alison Madueke. 
Alkalin kotun, Mai Shari’a Muslim Hassan yau Juma’a, ya amince da bukatar EFCC na a karbe kudin na wucin gadi tare da baiwa Diezanin makonni biyu ta yi bayani a kansu ko kuma a kwace su dindindin. 
Kudaden, wadanda suke dankare a cikin asusunan bankunan Sterling, First Bank da Access, ana zargin tsohuwar Ministar ta sace su ne tsurar su kuma kai tsaye daga asusun kmfanin mai na NNPC. Ana kuma zargin ta hada baki da wani mai suna Nnamdi Okonwo, tsohon shugaban Bankin Fidelity wajen yin aika-aikar. 
An dage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Janairun 2017 inda aka baiwa Diezani damar ta zo ta yi cikakken bayani ko kuma a mallaka wa Gwamnatin Tarayya kudaden.

You may also like