Kotu Ta Sa A Tsare Malam Idris Abdulaziz A Gidan Gyaran Hali
Kotu a jihar Bauchin Najeriya ta sa a tsare wani fitaccen Shehin Malami kuma limamin masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke jihar Bauchi Dr. Idris Abdulaziz a gidan gyaran hali bisa zarginsa da aikata kalaman batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W)

An kama shi bisa zargin shi da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad a lokacin da ya ke huduba a watan Ramadan.

Rahotanni sun nuna cewa jama’a da dama daga cikin al’ummar Musulmi a Jihar Bauchi ba su ji dadin kalaman malamin ba, wadanda suka kwatanta a matsayin abin Allah wadai da ban takaici.

Sakamakon haka, an tuhume shi da laifin tunzura jama’a da cin mutuncin ra’ayin addini, wadanda laifi ne a karkashin dokokin Najeriya.

Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a yankin. Wasu masu goyon bayan limamin sun ce yana amfani da ‘yancin fadar albarkacin baki ne, yayin da wasu kuma suka yi Allah-wadai da kalaman da ake zarginsa da yin kira da a hukunta shi.

Ana ci gaba da shari’ar, kuma har yanzu limamin yana tsare.

Lauyan Limamin Barista Umar Hassan ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya shaidawa manema labarai cewa wanda yake karewa ya gurfana a gaban wata kotun Majistare.

Alkalin ya ki amincewa da belinsa, sannan ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi har sai ranar Talata mai zuwa.

Masu lura da harkokin addini da na shari’a a Najeriya sun sanya ido sosai kuma suna ci gaba da bibiyar lamarin.

Yusuf AminuSource link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like