Wata kotun Babban birnin tarayya Abuja da ke zamanta a yanki Jabi ta sake kin bayar d belin matar nan da ta kashe mijinta, Maryam Sanda.
Kotun ta bayar da umarni a sake mayar da matar gidan kurkukun Suleja inda ake tsare da ita. Tun da farko dai, Maryam Sanda ta roki kotun kan ta bayar da belinta saboda tana dauke da juna biyu da mijinta, Marigayi Bilyaminu wanda dan tsohon Shugaban PDP ne, Bello Haliru.