Kotu ta soke haramcin sa hijabi a Lagos


Kotun daukaka kara da ke Lagos a Kudancin Najeriya, ta yanke hukunci cewa dalibai Musulmai na da damar sanya hijabi a matsayin kayan makarantarsu wato (Uniform).

Wannan hukunci ya soke hukuncin farko ne da wata kotun ta yanke na haramta sanya hijabin a matsayin kayan makaranta.

Alkalai uku daga cikin biyar din da suka yanke wannan sabon hukunci dai ba musulmai ba ne.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Musulunci MURIC, ta ce ta ji dadin wannan hukunci, kuma hakan “nasara ce ga tsarin shari’a a Najeriya”.

MURIC ta kuma yi gargadi ga jami’ai da kamfanoni masu zaman kansu, wadanda suke da halayyar muzgunawa mata Musulmai saboda suna sanya hijabi, da cewa su guji yin hakan.

Hukuncin da kotun ta yanke na haramta sanya hijabi a watan Oktobar 2013 ya jawo ce-ce-ku-ce a jihar, wadda take da yawan al’ummar Musulmai musamman daga kabilar Yarbawa.

Hakazalika kungiyoyin musulmi da dama sun nuna rashin gamsuwarsu da hukuncin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like