Babbar kotu dake Abuja a yau Talata ta tabbatar da Yahaya Bello a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kogi.
Kotun ta yi watsi da daukaka karar da Hon. James Faleke mataimakin Gwamnan da ya rasu Marigayi Abubakar Audu ya shigar da kuma abokin takararsa a jam’iyyar adawa ta PDP Kyaftin Idris Wada.
Rahoton ya kara da cewa, kotun za ta bayyana hujjojinta a ranar 30 ga Satumba 2016.