Kotu ta tasa keyar kanin Melaye zuwa gidan yarin Kuje


An tura Samuel Melaye, kani ga Sanata Dino Melaye ya zuwa gidan yarin Kuje dake Abuja.

Wata kotun Majistire dake zamanta a Mpape, Abuja ce ta tasa keyarsa ya zuwa gidan yarin bayan da aka gurfanar da shi gabanta inda ake tuhumarsa da hada baki wajen aikata laifi.

Yan sanda suna tuhumarsa tare da wasu mutane uku, Amaefufa David, Pius Inyang da kuma Muhammad Waziri bayan da aka bayyana sunansu cikin wadanda suka taimakawa Melaye ya tsere da hannun yan sanda.

An rawaito cewa Melaye ya yi tsalle daga motar yan sanda lokacin da take tsaka da tafiya akan hanyarta ta zuwa Kogi inda za a gurfanar da shi gaban kotu.

Dukkanin mutanen sun musalta zargin da ake musu.

Alkalin kotun ya dage shari’ar ya zuwa ranar 30 ga watan Afirilu domin ya saurari batun bayar da belinsu.

You may also like