Kotu Ta Tura Direban Da Yayi Yinkurin Kashe Gwamna Fayose Zuwa Gidan Yari 


Wata kotun majistire dake Ado Ekiti ta tura wani direba zuwa gidan yari kan zargin da ake masa na yinkurin hallaka gwamna Ayo Fayose na jihar. 

Yan sandan sun gurfanar da direban motar haya,  a ranar Laraba.Monica  Ikebuilo yar sanda mai gabatar da kara ta shaidawa kotun cewa mutumin da ake zargi ya aikata laifin a ranar 24 ga watan Satumba a layin Ejigbo a Ado-Ekiti.

Mai gabatar da kara tayi zargin cewa mutumin da ake kara a ranar da aka bayyana yayi yinkurin kisan Fayose ta hanyar dukansa da motarsa.

A cewar ta laifin ya saba da sashi na 320 na kundin dokar manyan laifuka  jihar Ekiti.

Kotun bata karbi rokon da lauya dake kare mai laifin,Felicia Nwandichi  tayi ba na a dage sauraran shariar na gajeren lokaci. 

Alkalin kotun, Dolapo Akosile, ta bada umarnin a cigaba da tsare mutumin da ake zargi da laifin a gidan yari har zuwa ranar 9 ga watan Oktoba. 

You may also like