Wata kotun majistire dake Ebute Meta a jihar Lagos ta ingiza ƙeyar wata mata zuwa gidan yari kan zargin zubawa danta tafasasshen ruwan zafi da yayivsanadiyar mutuwarta bayan da ta zargeshi da batar mata da kuɗi ₦200.
Matar da ake zargi mai shekaru 40 dake sana’ar sayar da kayayyaki ta gurfana gaban Babbar Majistire,Uwargida Oluyemisi Adelaja, kan zargin aikata laifin kisan kai.
Jami’in ɗan sanda me bincike Insifekta Chris Akpanomo ya shedawa kotun cewa matar da ake zargi ta aikata laifin ranar 8 ga watan Disamba a gida mai namba 670 dake kan titin Ikorodu a Owode Elede Ikorodu.
Ya yi zargin cewa matar da ake zargi ta aiki marigayin da ₦200 kacal da take da ita, domin ya siyo mata abinci amma ya dawo yace kuɗin sun bata.
A cewar Akpanomo cikin fushi ta watsa masa ruwan zafi ta kuma kulle shi a cikin gida inda ta cigaba da harkokin gabanta.
Ya kara da cewa ihun da yaron yayi tayi ne ya jawo hankalin makota inda suka garzaya da shi zuwa asibiti kafin daga bisani ya mutu a can.
Laifin ya saba da sashi na 222 na kundin manyan laifuka na jihar Lagos da ya siyaba hukuncin kisa ga wanda ya aikata irin laifi da ta aikata.
Alkalin kotun tayi umarnin a tura matar zuwa gidan yarin Ikoyi har sai ta samu shawara daga babban darakta dake kula da shigar da kara a jihar.
Ta kuma daga shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Janairu shekarar 2018.