Kotu Ta Umarci Kungiyar ASUU Ta Janye Yajin Aiki
ABUJA, NIGERIA – Mai shari’a Polycarp Hamman na kotun ma’aikata da ke birnin tarayya Abuja ne ya yanke hukuncin da ya bai wa kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU umurnin ta janye yajin aikin da ta ke yi kafin bangarorin biyu su warware rikicin da ke tsakaninsu.

Mai shari’a Hamman ya bayar da umurnin a mayar da karar da aka shigar ga shugaban kotun ma’aikatan Najeriya domin a mayar da batun ga wani alkali na daban.

Tuni dai dalibai suka fara bayyana jin dadinsu a gamę da umarnin kotun da ta ce malamai su koma bakin aiki. Hakazalika, su ma iyaye sun yaba da matakin kotun, ko da yake sun bayyana damuwa kan ta yiwu kungiyar malaman ta daukaka kara.

A ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2022 ne kungiyar ASUU ta tsunduma cikin yajin aikin gargadi da ya kai tsawon wannan lokacin, sama da wata 7 kenan.

Kotu dai ta hana kungiyar ASUU da mambobinta daukar wani mataki da zai sa su ci gaba da yajin aiki har sai an saurari karar da aka shigar a gaban babban alkalin kotun ma’aikatan.

Sai dai duk kokarin ji ta bakin kungiyar ASUU a kan matakin gaba da zata iya dauka ya ci tura.

Saurari rahoton Halima Abdulrauf daga Abuja Najeriya:

You may also like