Kotu Ta Umurci Gwamnati Ta Samarwa Dan Kasar China Da Ake Tuhuma Da Kashe Ummita TafintaGwamnatin jihar Kano ce ke tuhumar Mr Frank Geng da kashe Ummukulsum Sani wadda aka fi sani da Ummita. Mr Geng mutumin kasar China dake gudanar da harkokin sa na kasuwanci a Kano ya kasance daya daga cikin samarin Ummita.

Zaman Kotu

Zaman Kotu

Wani dalili ne dai da ba’a kai ga fayyacewa ba, ya kai shi ga hallaka budurwar tasa Ummita a gidan mahaifanta, ta hanyar caccaka mata wuka a kirjinta a daren ranar lahadi 17 ga watan jiya na Satumba, al’amarin da yayi sanadiyyar mutuwar ta nan take.

Da fari dai an gurfanar dashi ne a kotun majistire ta Kano dake Noman’s Land, amma saboda rashin hurumin sauraron irin wannan shari’a aka mayar da batun gaban babbar Kotun dake Miller Road a birnin Kano.

A makon jiya ne dai, kotun karkashin jagorancin mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ta so fara sauraron shari’ar, sai dai saboda rashin lauyan da zai kare Mr Geng, ya sanya ala tilas aka dage zaman shari’ar zuwa talatar nan 4 ga watan nan na Oktoba.

Koda yake lauyoyin bangarorin biyu sun bayyana a kotun a wannan karon, ba’a kai ga fara shari’ar gadan-gadan ba, saboda lauyan Mr Geng da ake tuhuma da kisan Ummita ya roki kotu ta bada umarnin samar da mai tafinta ga wanda yake karewa la’akari da cewa, turancin dayake iya Magana dashi bai kai ya kawo ba.

A hirar shi da Muryar Amurka, Barrister DanAzumi Abdullahi lauyan dake kare Mr Frank Geng yace dokokin Najeriya sun bada dama a samar da tafinta ga wanda ake tumama muddin baya jin harshen turanci, domin a fassara masa zuwa harshen daya fi fahimta.

Shi ma a nasa bayanin, Barrister Lawan Musa Abdullahi, babban Atoni na Kano kuma kwamishinan shari’a dake jagorantar lauyoyin gwamnati a wannan shari’a yace, su suka fara yunkurin neman tafintan saboda suna sane da cewa, dokar kasa da ka’idojin kotun sun bada dama ga Mr Geng tunda kamar yadda aa fada baya jin turanci sosai.

Tuni dai alkalin kotun Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya amince da waccan bukata ta lauyan dan China kuma ya bukaci ofishin jakadancin kasar China a nan Najeriya ya samar da mutumin da zai rinka aikin tafinta a yayin shari’ar domin Mr Geng da ake zargi da wannan kisan gilla ya rinka fahimtar mahawarar da za’a rinka yi a zauren kotun.

Daga bisani dai alkalin ya dage zaman kotun zuwa ranar 27 ga wannan wata na Oktoba domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Saurari rahoton a sauti:

You may also like