Wata kotun tarayya dake zamanta a Lagos ta kori dukkanin tuhume-tuhumen da akewa, Chimaroke Nnamani tsohon gwamnan jihar Enugu.
Hukumar Yaƙi Da Yiwa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati ta EFCC, ta tuhumi Nmandi da laifin naira biliyan ₦4.2 lokacin da yake riƙe da kujerar gwmnan jihar Enugu tsakanin shekarar 1999-2007.
An shirya gurfanar da shi gaban kotun a ranar Talata tun bayan da aka gurfanar da shi a shekarar 2007.
Ya yin zaman kotun na ranar, Ricky Tarfa Lauyan Nnamani ya sanar da kotun sakamakon rokon da yayi na sasantawa da hukumar ta EFCC a wajen kotu a watan Yuli na shekarar 2015.
Duba da ɓukatar da lauyan ya shigar kotun ta amince da yarjejeniyar da suka cimma inda ta soke dukkanin tuhumar da ake wa tsohon gwamnan.