Wata kotun tarayya da ke Abuja, ta yanke hukuncin daurin shekaru 105 ga wasu jami’an gwamnati biyu wadanda ke aiki ofishin Akanta Janar na tarayya bisa laifin yin amfani da matsayinsu wajen bayar da wasu kwangiloli ga wasu kamfanoni da suke da hannu a ciki.
Hukumar EFCC ce dai ta maka jami’an biyu; Mohammed Audu da Yusuf Ayedeji kotu wadanda ke kula da wani shiri da Bankin Duniya ke daukar nauyinsa kan inganta tsarin kashe kudaden gwamnati inda suka yi amfani da wannan damar wajen karya ka’idojin aikin.