Kotu ta yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame, hukuncin zaman gidan yari na shekara 14 ba tare da zabin biyan tara ba.
An gurfanar da Nyame a gaban kotun inda ake zarginsa da aikata laifuka 41 amma a karshe kotun ta same shi da aikata laifi 27 kadai.
Kotun ta dorawa gwamnan alhakin yin sakaci da kudaden gwamnati da kuma yin amfani da ikonsa na gwamna ba kamar yadda doka ta tanada ba.
Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC ita ce ta kai karar gwamnan gaban kotu a shekarar 2007 inda take zarginsa da salwantar da kudaden da yawansu ya kai naira biliyan N1.64 lokacin da yake kan kujerar gwamnan jihar tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.
Hukumar EFCC ta gabatar da shedu da dama da suka tabbatar da cewa Nyame ya bada umarnin karkatar da kudade sama da miliyan N 345 ya zuwa wani kamfani mai suna Saman Global cikin makonni biyar a shekarar 2005.
Shari’ar ta samu tsaiko ne bayan da tsohon gwamnan ya shigar da kara gaban wata kotun inda yake kalubalantar hurumin kotun na sauraran shari’ar.
A shekarar 2016 kotun koli ta kasa ta yi watsi da daukaka karar da ya yi inda ta ce kotun tana da hurumin sauraran karar hakan ne ya bawa kotun damar cigaba da sauraran shari’ar har ta kai ga yanke hukuncin na yau.