Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Kisa Kan Laifin Satar Naira 3,420Babbar kotun jihar Osun dake zamanta a Osogbo ta yankewa wani mutum mai shekaru 40, Kayode Adedeji hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin yiwa wata mata fashin kudin naira 3420.

An yankewa Adedeji hukuncin ne a ranar Laraba04 duk da cewa ya aikata laifin a ranar 25 ga watan Afirilun shekarar 2009.

Lauya mai gabatar da kara daga ma’aikatar shari’ar jihar Elizabeth Ajayi  ta fadawa kotun cewa, Mista Adedeji yayi wa wata Omowumi Adebayo,dake  Bolorunduro a yankin Ilesa fashin kudinta.

Mai gabatar da karar tace dan fashin yana dauke da muggan makamai lokacin da yaje aikata fashin a gidan matar da daddare.  

An rawaito cewa Adedeji ya tsere bayan ya aikata fashin amma yan kungiyar OPC sun bishi inda suka samu nasarar kama shi.

Yaki yarda ya amsa laifin fashi da makami da ake tuhumarsa sa da shi lokacin da aka gurfanar dashi shekaru takwas da suka gabata kafin a bada belinsa. 

A cewar Adedeji wanda ake zargin ya saba ka’idar belin ta hanyar aikata laifi makamancin haka wanda ya jawo aka turashi gidan yari dake Ilesa.

Alkalin dake sauraran karar Kudirat Akano ta samu Adedeji da aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa kuma ta yanke masa hukunci. 

Lauyan dake kare wanda ake kara ya roki kotun da tayi sassauci kan hukuncin  amma kotun tayi umarni da akashe Adedeji ta hanyar rataya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like