Kotu Ta Yi Watsi Da Diyyar Bilyan Biyu Da Patience Jonathan Ta Nema Daga EFCC


Wata kotun tarayya da ke zamanta a Babban birnin tarayya Abuja ta yi fatali da bukatar da Uwargidan Tsohon Shugaban Kasa, Patience Jonathan ta nema kan hukumar EFCC ta biyata diyyar Naira Bilyan biyu bisa abin da ta kira keta hakkinta na dan Adam.

A watan Yuni na shekarar da ta gabata ne dai, lauyan Uwargidan Shugaban kasar, Barista Ifedayo Adedipe ya shigar da kara kotun inda ya zargi EFCC da kokarin cin zarafin Patience Jonathan saboda ta fito fili ta nuna adawa da takarar Shugaba Muhammad Buhari a kakar zaben 2015.

You may also like