Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Murtala Nyako Na Neman A Mayar Da Shi Gwamnan Jihar Adamawa


4bkc1ef32b7706jgxm_800c450-1

 

 

Kotun kolin Nijeriya ta yi watsi da bukatar da tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako ya gabatar mata na yana bukatar da ta mayar da shi kan kujerarsa don ya karasa wa’adin mulkinsa bayan tsige shi da da ‘yan majalisar dokokin jihar suka yi.

A hukuncin da alkalai bakwai na kotun kolin karkashin jagorancin mai sharia Tanko Muhammad suka fitar a yau din nan Juma’a, sun ce sun yi watsi da bukatar da Nyako ya gabatar na a mai da shi kan kujerar tasa ne saboda shi da kansa ya cire wannan bukatar cikin karar da ya shigar gaban kotun daukaka karar wacce ta yanke hukuncin cewa ba za a mai da shi kujerar tasa ba duk kuwa da cewa tsige shi da aka yi din bai dace ba. Don haka Alkalan suka ce su ma a nasu bangaren ba za  su mayar da shi ba.

A ranar 15 ga wan watan Yulin shekara ta 2014 ‘yan Majalisar dokin jihar Adamawan suka tsige shi daga kujerar shugabancin jihar watanni goma kafin ya kammala wa’adinsa. ‘Yan majalisar sun tsige shi ne bisa laifin saba ka’idar aiki da almubazzaranci da dukiyar al’ummar jihar.

A watan Fabrairun da ya gabata ne dai kotun daukaka karar da tsohon gwamna Nyako ya kai mata kuka ta yanke hukuncin cewa ba a bi ka’ida ba wajen tsige tsohon gwamnan amma dai ba za a iya mayar da shi kan kujerar ta sa ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like