Kotu ta zartar da hukuncin ɗaurin shekaru 60 kan kwamandan Boko Haram mai shekaru 22


Babbar kotun tarayya dake Kainji jihar Niger ta yankewa Abba Umar wani kawamanda a ƙungiyar Boko Haram ɗaurin shekaru 60 kan aikata ta’addanci.

Gwamnati ce ta gurfanar da shi gaban kotu tana tuhumarsa da aikata laifuka biyar.

A zaman kotun na ranar Talata, Umar wanda aka kama bayan ya yi yunkurin kai harin ƙunar ɓakin wake da bai samu nasara ba a Gombe a shekarar 2014. Ya tabbatar da cewa hotunansa tare da bom din da yake dauke da shi da mai gabatar da ƙara ya nuna masa a matsayin sheda na gaske ne.

Kwamandan wanda ko kaɗan bai nuna alamar dana-sani ba ya fadawa kotun cewa idan har aka sake shi to zai cigaba da aikata ta’addanci a dajin Sambisa.

Ya kuma bayyana cewa akwai mutane kusan ɗari da suke ƙarƙashinsa.

Da yake zartar da hukuncin, alƙalin ya zartar da hukuncin mara tsauri akan Umar.

Biyu daga cikin tuhuma biyar da akewa Umar na ɗauke da hukuncin kisa amma alƙalin yace ya rage hukuncin ne saboda cusa masa ra’ayin  ƙungiyar addinin da aka yi ne yasa yake haka.

 

You may also like